'Yan Bindiga Abuja Hausa Labarai Labarai daga Jihohi Mahara Najeriya News PREMIUM TIMES

‘Yan BINDIGA: ‘Yan sanda biyu sun rasu, mahara da dama sun sheka lahira a Zamfara

Written by Tabarau

Kakakin rundunar’ Yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an ‘Yan sanda biyu sun rasu a batakashi da yan sanda suka yi da gungun mahara a Magami, karamar hukumar Gusau.

Muhammed ya ce yan sandan sun kai wa mutanen Magami dauki ne bayan an sanar da su cewa wasu gungun mahara sun afka garin bisa babura.

Ko da jami’an ‘yan sanda suka isa garin Magami sai aka fara dauki ba dadi a tsakanin su.’ Yan sanda sun yi nasaran kashe mahara da dama, sannan wasun su sun arce da rauni a jikinki.

Mohammed ya ce, sai dai kuma suma ‘Yan sandan sun rasa jami’ ai biyu.

A karshe dai ya ce, kwamishinan ‘Yan sandan jihar ya aika da karin jami’ ai a wannan yanmi domin samar da tsaro gudun kada maharan su sake dawowa.

KARANTA:  Ministan Gona Nanono ya angwance da 'yar shekara 18

Leave a Comment