ZANGA-ZANGAR NLC: Majalisar Dokokin jihar Kaduna ba ƴan amshin shata ba ne kawai, har da Ɗankwairo, Daga Fareeda Isma’il

Tun da nake ban taba ganin majalisar jihar da take a lalace, kamar majalisar jihar Kaduna a yanzu ba. Tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a kasarnan a 1999, majalisar Kaduna ke kan gaba wajen nuna bajinta a harkar majalisa.

Babu ma kamar lokacin gwamna Ahmed Makarfi. A wannan lokaci an yi jajirtattun ƴan majalisa da kan taka wa gwamna birki wanda ya kai ga wasu ma an yi ta kai ruwa rana da su, wasu har hakan ya sa sun rasa kujerar su ta shugabancin majalisar jihar amma yanzu yadda kasan dakin asibiti shiru.

Majalisar jihar Kaduna ta zama kamar ɗakin asibiti, tsit, kowa na kwance ba ka jin komai na fitowa daga majalisar.

Wasu lokuttan ma sai ka yi tambaya an ya majalisar Kaduna na aiki kuwa ko suna hutu ne.

A irin gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna mai kurin cewa shi ɗan boko ne, ya karantu kuma da masu ilimi yake aiki ba a taba tunanin da kansa zai yi aiki da kakakin majalisar na yanzu ba. Amma ya yi buris saboda ya san zai iya juya shi yadda ya ke so ba tare da a samu wani cikas ba. Da yake kakakin da ya waye kuma shima ya san menene duniya ai ya kasa aiki da shi, dole aka yi kutunkutun din tsige shi a majalisar.

KARANTA:  Hukumar NDLEA ta kama gidajen yin buredi da ke hada garin fulawa da ganyen Wiwi

Babu abinda ya fi cimin tuwo a kwarya kamar yadda koda ace layi ɗaya ce ta sanarwa akan Zanga-zangar Ƙungiyar Kwadago da ta yi a Kaduna.

Har majalisar sun je amma, ko dan majalisa daya bai iya fitowa ya yi wa masu zanga-zanga jawabi ba koda ko karya ce zai faɗi.

Haka aka yi ta kai ruwa rana da masu zanga-zanga, ƴan jiha na fama da kansu na rashin wuta da sauransu amma zaɓaɓɓun ƴan majalisar jihar sun tafi sun ɓoye abin su.

Ya dai kamata su yi karatun ta natsu su fito su ba maraɗa kunya su yi abinda mutanen su suka aika su su yi a majalisa, su rika tunkarar fannin zartas wa da kuma kyamatar abinda bai kamata ace anyi a jihar ba.