Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Ibrahim Attahiru ya rasu a hatsarin jirgin sama a Kaduna

Rahotanni daga PRNigeria ya nuna cewa babban hafsan sojojin Najeriya, Ibrahim Attahiru ya rasu a hadarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.

Jaridar ta ruwaito cewa, dakaren ya rasu tare da wasu jami’an soji da ke tare da shi a hadarin da ya auku a dalilin ruwan sama da ya da ka yi a Kaduna.

Janar Attahiru ne ya maye gurbin tukur Buratai bayan Murabus da yayi a cikin wannan shekara.

KARANTA:  LIKITOCI: Aikin korona ya kashe mana likitoci 17, shi ya sa muka shiga sahun yajin aiki –Shugaban Likitocin Badun