Abin sha Hausa Labarai Maltina Nishadi PREMIUM TIMES

Yadda ake hada abin sha mai dadi da gamsarwa da Maltina cikin dan kankanin lokaci

Written by Tabarau

Sanin kowa ne cewa idan nishadi ake bukata kuma ake so aji aji musamman idan a na bukatar jika makoshi a kuma gamsu, babu kamar a kwankwadi Maltina.

To yanzu garin dadi ya zo kusa domin da Maltina za a iya hada abin sha don samu nishadi da kuma burge iyali da baki a koda yaushe.

Bai tsaya ga baki da iyalan gida ba, hatta yara za a iya hada musu wannan abin domin su sha a gida da kuma a makaranta lokacin Tara.

Yadda ake hada wannan abin sha

1 – Za a samu ‘Ice Cream’ mai dandanon Vanilla sai a dibi kamar babban cokali uku zuwa hudu a saka a cikin kofin nika na zamani.

2 – Daga nan sai a zuba karamin cokali na sinadarin ‘Vanilla essence’.

3 – Sai kuma a kara da karamin cokali na sinadarin ‘Chocolate essence’

4 – Sai kuma a dildila  rabin kwalba na Maltina a cikin wannan kofin nika.

Bayan an yi haka sai a markada shi duka gaba daya, wato a nike shi.

Daga nan sai shan lagwada.

Za a zuba shi ciki kofi ko kuma kwano, sannan za a iya kara masa ‘Ice cream’ mai dandanon ‘Vanilla’ a sama kafin a sha.

KARANTA:  A yi sallar Idi a masallatan Juma'ar unguwanni, babu zuwa filin Idi

Leave a Comment