Abuja Babban Labari Najeriya Nasarawa PREMIUM TIMES Suke

Gwamnan Sule na jihar Nasarawa ya siya wa sarakunan jihar motocin kasaita biliyoyi naira

Written by Tabarau

Kowa dai da abin da ya dame shi. A daidai gwamnatin Kaxuna na fama da karauniyar rage ma’aikata don ta samu kudin gina tituna da kirkiro hanyoyin tara kudade a jihohi da gwamnatoci ke yi, A jihar Nasara wa kuwa watandan motocin kasaita gwamnan jihar Nasarawa ya yi wa manyan sarakunan jihar.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa gwamnan ya siya wa manyan sarakuna kalla 26 motocin kasaita wanda kudaden su ya fara daga naira miliyan 50 zuwa sama ne.

Gwamnatin jihar ta koka kan karancin kudade musamman wadanda za a rika biyan kudaden ma’aikatan jihar.

Masu yin fashin baki a harkar siyasa da tattalin arziki sun ce wannan ba lokaci bane na kashe irin wadannan kudade don faranta wa sarakuna rai haka kawai da motoci masu tsada irin haka.

” Jihar Nasarawa na daga jikin jihohin kasar nan da ke samun kaeancin kudaden shiga harda na kason gwamnatin tarayya. Idan har gwamna zai iya dibar tsabar kudi irin haka ya siya wa saeamuna motoci, lallai bai yi nazari mai zurfi ba.

Kamata ya yi idan ma babu abinda za ayi da su ne a ajiya su domin bacin rana. Idan kuma dole sai an siya wa sarakunan motoci akwai motoci daidai kima, wanda a ganina ma ba abu ne da ake bukara kashe wa kudi haka ba.

KARANTA:  Ma’aikatan Kotu da Ma’aikatun Shari’a na kasar nan sun sheka yajin aiki

Leave a Comment