Fursinoni 115 sun ci darussan Turanci da Lissafi a Jarabawar NECO na bana

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen yari ta kasa dake jihar Enugu Monday Chukwuemeka ya bayyana cewa wasu fursinoni 115 sun ci darussan Turanci da lissafi a jarabawar NECO na shekarar 2020 da aka yi a jihar.

Chukwuemeka ya fadi haka a garin Enugu a zantawa da yayi da manema labarai.

Hukumar jarabawar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar ranar 7 ga Mayu 2021.

Chukwuemeka ya ce a shekarar 2018 fursinoni 84 ne suka ci darussan Turanci da Lissafi, kuma a shekarar 2019 fursinoni 136 ne suka ci darusan Turanci da lissafi a jihar.

Ya ce hukumar gidan yari na horas da fursinoni da koyar da su karatun boko a lokacin zaman su a gidajen.

KARANTA:  Majalisar Dattawa ta ki amincewa da naɗin Lauretta Onochie a matsayin kwamishina a hukumar zaɓe