Abuja Babban Labari El-Rufai Najeriya News PREMIUM TIMES

Mun yi shirin yi wa ‘yan bindiga luguden bama-bamai kafin suka sako daliban Afaka

Written by Tabarau

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa saura kiris dakakrun Najeriya su hallaka ‘yan bindigan da suka sace daliban Afaka da ruwan bama-bamai kafin Allah ya ceto su.

El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabin da yayi a taron ‘African Leadership Group’.

” Dole za a rasa wasu dalibai amma kuma hakan ya fi mana maimakon mu biya su kudin fansa. Idan aka yi musu ambaliyar bama-bamai za a kashe dukan, kuma za a ceto wasu daliban da ran su ke gaba maimakon mu biyan kudin fansa.

” Mun san lallai akwai hadari, amma kuma muka yarda hakan za a yi saboda, a irin wannan yaki dole a rasa wasu muddun ana so a yi nasara akai.

El-Rufai ya nanata a lokutta da dama cewa shi ko gwamnatin sa ba za su biya kudin fansa akan kowani mutum da ‘yan bindiga suka sace ba. Ya ce ko da ko dansa aka sace, sai dai su yi sallama da shi, sannan yayi masa fatan Allah ya hada su a Aljannah, amma ba zai biya su ko sisi ba.

Mahara sun saki ‘yan makarantar gandun Daji 27 dake tsare da su a daji kwanaki 55 bayan suna tare da su.

KARANTA:  Maimakon Buhari ya maida hankali kan matsalar tsaro, ya zauna karbar ’yan yawon gantali cikin APC –Fayose

Tuni dai har an hada daliban da iyayen su ranar Juma’a.

Leave a Comment