Abuja Hausa Kiyawa Labarai Labarai daga Jihohi Najeriya News PREMIUM TIMES

KANO: ‘Yan sanda sun damke matasa biyu dake fashin Atamfofi a Dawanau

Written by Tabarau

Wasu matasa biyu, Sanusi Ahmed da Rabiu Abubakar sun shiga hannu bayan kama su da jami’an ƴan sandan Kano suka yi suna haurawa gidajen mutane suna yi musu fashin Atamfofi da wasu kayan.

Kakakin rundunar Kano, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a bidiyo da ya saka a shafin sa daka Facebook ranar Asabar.

Kiyawa ya bayyana cewa bayan kararraki da mazauna unguwar Dawanau suka rika kaiwa ofishin ƴan sanda karin samun yawa-yawan matasa masu fashi suna tsallakawa gidaje suna satan kaya, jami’an suka fantsama farautar su.

Sanusi da Rabiu sunce bayan zannuwa da suke kwacewa sun saci batirin Sola a gidan wani.

An nunu wasannan barayin rataye da zannuwan, bindiga kirar hannu da sharbebiyar adda wanda suke tsorata mutane da su, idan ka ki bada hadin kai kuma su aikata maka.

KARANTA:  GARGADIN EL-RUFAI: Ka garzaya ka biya harajin gidan ka ko ya fada cikin gidajen da gwamnati za ta yi gwajon su

Leave a Comment