Abuja Hausa Hodar Ibilis Labarai Najeriya News PREMIUM TIMES

An damke wanda ya yi ‘kashin’ kullin hodar Ibilis 59 a filin jirgin saman Abuja

Written by Tabarau

Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta kama wani matashi mai suna Okoguale Douglas da ya rika sako kashin kulli hodar ibilis har kulli 59 a filin jirgin saman Abuja.

A lissafe dai nauyin hodar ibilis da douglas mai shekaru 23 da ya sassako ya kai gram 781.2.

Jami’in yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a.

Ya ce NDLEA ta kama wannan matashi yayin da yake kokarin shiga jirgi kasar Italy daga Najeriya.

“Binciken da NDLEA ta gudanar ya nuna cewa Douglas ya hadiye kulin muggan kwayoyin ne inda dole suka tilasta shi ya yi bahayansu.

Babafemi ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa Douglas ya fara zama a kasar Italy a shekaran 2011 tare da ‘yan uwan mahaifinsa.

Ya ce Douglas ya dawo Najeriya ranar 4 ga Afrilu domin yin jana’izan mahaifin da ya rasu kwanannan.

“Douglas ya ce ya karbi hodar ibilis din ne a Abuja wajen wasu mutane da Bai taba ganin su ba, zai kai musu kasar Italiya.

KARANTA:  Yadda na shafe kwanaki 25 a hannun Fulanin da su ka yi garkuwa da ni - Wazirin Dansadau

Babafemi ya ce hukumar za ta ci gaba da yin bincike domin gano sauran mutanen dake da hannu akai.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda NDLEA ta kama hodar ibilis mai nauyin giram 140 da aka boye a gunkin ‘Mary’ wanda ake inkari da ita ce mahaifiyar Yesu.

Darikan Katolika na amfani da gunkin Mary mahaifiyar Yesu wajen yin adu’o’i domin a wurin su Mary ita ce ta haifo mai ceton su.

Sai dai wannan karon wasu kangararrun mutane sun dirka wa gumakan Mary din kwayoyi domin yin safarar su zuwa kasashen waje.

Hukumar NDLEA ta kama gunkin a tashar jiragen saman Abuja a hanyar waske wa da su kasar Philippines.

Leave a Comment