Abuja Hausa Labarai Najeriya News PREMIUM TIMES Wasanni

Cutar mu aka yi, amma mun fi karfin Chelsea – In ji magoya bayan Madrid

Written by Tabarau

Mabiya bayan Kungiyar kwallon kafan Real Madrid musamman Najeriya sun yi korafin wai alkalin wasa ne ya murde musu wasa ya ri rika baiwa Chelsea dama har ta yi nasara a kan su.

Chelsea da yi ragaraga da Madrid a wasan kusa da kashe na gasar Champions League da aka buga a filin Chelsea dake Ingila.

Dama kuma a wasan farko da aka buga a Madrid, kasad Spain, Chelsea da buga Kunnen doki da Madrid.

Wa haduwa ta biyu, Chelsea ta nuna wa Madrid ba sani ba sabo, domin tun a tashin farko ta ruka kai wa Madrid Luguden hare-hare a ragar ta kafin a karshe baya duk ta gama birkita kwakwalwarta sai kwallo daya ta shiga.

Gab da za a tashi wasa kuma kwallo ta biyu ta shiga.

Kurunkus, kungiyar Chelsea da Manchester City za su buga wasan karshe a karshen wannan wata.

KARANTA:  CBN na da ikon buga kudade ta ramta wa Gwamnatocin Jihohi - Emefiele

Leave a Comment