Ina rokon kungiyar Miyetti Allah ta sa baki a sako daliban Kaduna – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya yi kira ga kungiyoyin MACBAN da na Miyetti Allah su wa Allah su saka baki a sako daliban manyan makarantun Kaduna dake tsare a hannun Mahara.

Sanata Sani ya kara da cewa lallai gwamnati ta dauki gargadin maharan da muhimmanci domin da gaske suke daga yadda shugaban kungiyar ya ke bayani.

Lallai a san yadda za a yi a ceto wadannan yara tun kafin su kwararo mana gawarwaki 17 na yaran da ke tsare a wajen su.

Duk lokacin da aka sace dalibai ba za ka ji komai a kai ba sai annsako su ko kuma an aiko da gawar wanda suka kashe. Ina jami’an tsaron mu na sirri?

Idan muna cewa ba za mu biya kudin fansa ba, toh me jami’an tsaron mu suke yi wajen ganin sun ceto yaran daga hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da su.

Ƴan Najeriya na cigaba da rokon gwamnati ta biya kudin fansan domin a saki daliban wadannan makarantu biyu dake Kaduna.

A yau Talata iyayen daliban makarantar koyon aikin gona da gandun daji dake Kaduna sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, suna rokon majalisar ta kawo musu dauki a sako ƴaƴan su da suka shafe kwanaki 55 a tsare.

KARANTA:  Dalilin da ya sa aka daina kashe wa Hukumar Yaƙi da Rashawar Kano kuɗi -Gwamnatin Kano