GARGADIN TINUBU: “Idan Najeriya ta tarwatse sai mun fi Iraqi da Sudan lalacewa”

Babban jigon jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya yi kakkausan gargadin cewa masu tayar da jiniyoyin wuya su dauki darasi daga bala’in yakin Basasa da aka yi a kasar nan a baya da kuma wasu yake-yaken da su ka kassara manya da kananan kasashe.

Da ya ke jawabi wurin taron addu’o’in Tafsirin Ramadan da aka shirya a Gidan Gwamnatin Jihar Lagos, Tinubu ya ce an shirya addu’o’in don nemar wa Lagos da Najeriya zaman lafiya.

Ya ce Allah ba zai biya wa masu son Najeriya ta tarwatse bukatun su ba. Kuma ya ce ya kamata masu neman tayar da zaune tsaye su tuna cewa har yanzu Najeriya ba ta gama fita daga bala’in Yakin Basasa ba.

“Kada Allah ya kawo tarwatsewar kasar nan, domin ni dai idan kasar nan ta tarwatse, to ba ni da wani wurin da zan koma na ci gaba da rayuwa da harkoki na.

“Ya kamata tsagerun da ke tayar da jijiyoyin wuya su sani cewa zaman mu kasa daya tare da juna shi ne mafi alheri gare mu baki daya.

KARANTA:  ALAKA DA 'YAN BINDIGA: Masarautar Katsina ta tsige Hakimin Kankara

“Shi yaki idan ya barke, ba a rana daya ya ke karewa ba. Zai dauki tsawon lokaci, sannan kuma za a shafe shekaru masu yawa ana cikin wulakantacciyar rayuwa.

“Idan Najeriya ta tashi lalacewa, sai ta fi kasashen Iraki da Sudan lalacewa. Kuma za ta shafe tsawon shekaru cikin halin kunci ta kaka-ni-ka-yin da babu wanda ya san ranar fita.”