KORONA: Wadanda suka yi allurar rigakafi za su iya yawo ba tare da takunkumin fuska ba

A dalilin samun raguwar yaduwar cutar korona gwamnatin kasar Amurka ta umarci duk wadanda suka yi allurar rigakafin korona cewa za su iya yawo ba tare da takunkumin fuska ba.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka CDC ta sanar da haka ranar Talata.

Bisa ga sabbin sharuddan guje wa kamuwa da cutar da hukumar ta fitar sun nuna cewa wadanda suka yi allurar rigakafin za su iya zama a cikin taron mutane wanda babu yawa sosai.

Shugaban hukumar Rochelle Walensky ta ce bisa ga wannan sanarwa mutane sun samu sauki wajen ci gaba da gudanar da harkokinsu na rayuwa kamar yadda suka saba yi a baya.

Sabbin dokokin guje wa kamuwa da cutar Korona.

Walensky ta ce wadanda suka yi allurar rigakafin korona za su iya zama a cikin taron mutane ba tare da sun saka takunkumin fuska ba, inda a kwai iska yana shiga yana fita ko kuma ma a waje.

Ta ce an tsananta amfani da takunkumin fuska domin dakile yaduwar cutar amma bincike ya nuna cewa wadanda suka yi allurar rigakafin ba su iya yada cutar ba.

KARANTA:  TSANANIN KISHI: An yi jana'izan Amarya Fatima da Kishiyarta ta kashe a Minna kwanaki 54 bayan aure

Zuwa yanzu mutum kashi 42% na mutane a Amurka sun yi allurar farko na rigakafin Korona.

Sannan sama da kashi uku na yawan mutanen dake Amurka sun yi allurar rigakafin Korona.

Sakamakon binciken ‘Worldometers’ ya nuna cewa mutum miliyan 32 sun kamu da cutar sannan mutum 500,000 sun mutu a Amurka.