Yadda ake neman gafara a wajen Allah, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Neman Gafara, wato Tuba wajibi ne ga bawa kuma cikin gaggawa ake yi batare da jinkiri ba. Ana Tuba ne ta hanyan (Istigifari) neman Gafara ga Allah. Duk bawan da ya Tuba, Tuba na gaskiya, kuma ya nemi Gafarar zunubin sa, wato ya yi Istigifari, to, Allah zai gafarta masa, komai girman zunuban sa. Ya ku wadan da ku ka yi Imani! Ku Tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya. (Suratul Tahrim aya ta 8).

A wajen neman gafaran laifin ko sabon ko zunubin da yake tsakanin bawa da Ubangijin sa, mutum zai bi wadannan matakai:

1) Yankewa daga laifin ko zunubin da bawa yake yi. Wato daina mummunan laifin da mutum yake aikatawa na sabon Allah, a lokacin da ya keda dama da ikon cigaba da laifin, sai ya daina, don jin tsoron Allah. Ba a lokacin da laifin ya fi karfinsa ba.

2) Yin nadama da kuma danasani akan laifin.

3) Kudurcewa ba zai kara aikata wannan laifin ba, har karshen rayuwar sa, da tsayuwa akan hakan.

KARANTA:  GABA KURA BAYA SIYAKI: Yadda manoman da Boko Haram su ka raba da gonakin su ke rayuwar ƙunci a Sansanonin Gudun Hijira a Barno

4) Neman gafara (Istigifari) daga Allah a kan laifin da rokonsa yafeya.

5) Nisantar mutane da gurare da duk abun da yake kusantar da mutum zuwa ga wannan laifin.

Amma idan laifin ya kunshi sabawa Allah, ta hanyan shiga hakkin wani bawan, to, wannan ya shiga cikin hakkin bawa tsakanin sa da dan-uwansa, to zai kara akan na baya tare da waddanan, a wajen neman gafaran laifin da ya ke sabon Allah ne da ya shafi hakkin wani:

1) Mayar da hakkin da yake kan sa, zuwa ga mai ita, in dukiya ce ko wani kaya ko dukkanin wani abinda za’a iya mayarwa.

– Idan babu abin, to, sai a mayar da kimar sa.

– Idan mai hakkin ya mutu, to, a mayar ma magadan sa. in kuma ba’a sanshi ba, ko ba za’a iya gano inda yake ba, to a yi masa sadaka da shi, da niyyar Allah ya kai ladan agareshi.

2) In hakkin ba na dukiya ba ne, kamar cin nama ko annamimanci ko kazafi ko sharri ko zalunci ko wata cutarwa, to, dole ne ya nemi yafiya da gafara daga wanda aka zalunta.

KARANTA:  Hadarin Jirgin Saman Hafsoshin Sojan Najeriya: Ya Zama Wajibi Ayi Kwakkwaran Bincike Na Gaskiya, Daga Imam Murtadha Gusau

– Amma fa sai in ya kasance neman yafiyan ba zai haifar da wata fitinar ba.

– Idan zai hafar da fitina, to, sai mutum ya kyautata, ya kuma gyara duk abinda ya bata.