DPO Kebbi Labarai daga Jihohi Mahara Najeriya PREMIUM TIMES

KEBBI: Yadda barayin shanu su ka bindige DPO, ‘yan sanda takwas da dan bijilante a Sakaba

Written by Tabarau

‘Yan bindiga sun bindige DPO na ‘yan sandan Karamar Hukumar Sakaba fa ke Jihar Kebbi da kuma wasu ‘yan sanda takwas a ranar Lahadi.

Haka kuma maharan sun bindige wasu ‘yan bijilante biyu, kamar yadda Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ya shaida wa PTEMIUM TIMES, cewa cikin dare aka kai harin da ya yi asarar rukanan jami’an tsaron.

Maharan dai an hakkake daga Jihar Zamfara da Neja su ke tsallakawa Kebbi su saci shanu ko koma cikin dazukan da su ka fito.

Sun fitini garuruwan Kunduru, Bajida da Rafin Gora da sauran garuruwan da ke kusa da sakaba.

Ganau ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun rika bi gari-gari su na satar shanu su na tarawa Sakaba.

Sakaba ta yi iyaka da jihar Zamfara da jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce Kebbi na cikin tashin hankalin tsoron kada hare-haren ‘yan bindiga ya hana dimbin manoma da yawa aure.

Hakan kuwa zai iya haifar da tsadar kayan abinci a Arewacin Najeriya.

KARANTA:  NIMONIYA: Rashin isassun kayan aiki a asibitoci na cikin matsalolin dake kisan yara a jihar Jigawa - Kungiya

Leave a Comment