Talauci da fatara suka sa Edris Abdulkarim ya rangada wakar kiyayya ga Buhari – Keyamo

Karamin ministan Kwadago, Festus Keyamo ya tona asirin mawaki Edris Abdulkareem cewa ya rika bi yana maula a taimakeshi da kudi cewa ya talauce ba shi da kudi.

Keyamo ya maida wa Edris martani ne bayan ya yi masa habaici a cikin sabuwar wakar da yayi wanda maimaici ga wanda ya taba yi a lokacin mulkin Obasanjo, mai taken ‘Nigeria Jagajaga’.

A cikin wakar, Edris ya rika sukar gwamnatin Buhari inda ya ke tuna wa masu saurare arangamar masu zanga-zangar EndSars da jami’an tsaro a mashigar Lekki, wato Lekki toll gate.

Keyamo ya ce ” tun a lokacin Kamfen a 2019, Edris ya rika kira na ya na aika mini da sakonni cewa yana so in saka shi cikin tafiyar Buhari ko zai dan samu ‘yan kudi domin ya talauce, sannan kuma dan sa bashi da lafiya.

” Daga baya Edris ya rika aika min da sakonni, har ya kai ga ya na so wai in taimaka mishi in hada shi da ministan Shari’a Abubakar Malami, Amaechi da wasu jiga-jigan gwamnati da jam’iyya. Haka dai bai barni na sha iska ba, ya roki wai in bashi naira miliyan 1.3 zai biyan kudin Otel din sa da kuma kudin asibiti.

KARANTA:  RASHIN TSARO: Kungiyoyi 120 sun nemi a fito a yi zanga-zanga, kuma a kaurace wa shagulgulan Ranar Dimokradiyya

Daga baya wani babban jami’in gwamnati ya gaya min wai ya yi ta bibiyarsa yana mika kokon barar sa ya taimaka masa da kudi, yan cikin kangingin talauci, sannan mahaifiyar sa bata da lafiya. haka dai ya rika bi ya maula a tsakanin mutane.

Dalilin kin samun shiga da baiyi ba, shine ya koma ya yayi wannan waka don ya ci mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari.