RANAR ZAZZABIN CIZON SAURO: Za a bukaci naira Tiriyan 1.89 don dakile yaduwar cutar a Najeriya – Minista Ehanire

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa Najeriya za ta bukaci naira Tiriyan 1.89 domin dakile yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a kasar nan.

Dakile yaduwar cutar ya hada da rage yaduwar cutar da kashi 10% da rage yawan mace-macen da ake samu a dalilin cutar zuwa kasa da kashi 50% daga cikin yara 1000 da ake haihuwa a kasan.

Ehanire ya fadi haka ne a taron shirin ranar taron cutar zazzabin cizon sauro ta shekaran 2021 da aka yi a Abuja ranar Juma’a.

Ministan ya ce gwamnati ta tsaro wasu tsauraran matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Ya ce bisa ga lissafi zantar da wadannan matakai zai ci Naira tiriyan 1.89 sannan zantar da matakan a cikin wannan shekara zai ci Naira biliyan 352.

Ehanire ya ce kashi 63.1 na kudaden da gwamnati za ta bukata za a yi amfani da su wajen siyo magunguna, inganta aiyukkan jami’an lafiya domin samar wa mutane kiwon lafiya ta gari a farashi mai sauki.

Ya kuma ce za a yi amfani da kashi 35.9 wajen gudanar da bincike domin gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar.

KARANTA:  HUDUBAR SABON SUFETO JANAR: Kada ƴan sanda su sake barin ƴan iska su banka wa ofisoshin su wuta

Bayan haka Ehanire ya yi kira ga kungiyoyin bada tallafi da fannin dake zaman kansu da su mara wa gwamnati baya wajen yaki da cutar musamman yadda gwamnati bata da wadannan kudade da ake bukata a ƙasa.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kebe ranar 25 ga Afrilu domin ganin ci gabn da aka yi wajen dakile yaduwar Zazzabin cizon sauro sannan da tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen ganin bayan cutar a duniya.

Taken taron bane shine ‘An ja layin daga domin ganin bayan zazzabin cizon sauro’.

WHO ta zabi wannan take ne domin karfafa gwiwowin kasashen duniya wajen yaki da cutar.

Zazzabin cizon sauro

Zazzabin cizon sauro cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cizon sauro.

Alamun ta sun hada da zazzabi, ciwon Kai, rashin iya cin abinci, ciwon gabobin jiki da sauran su.

Cutar na iya yin ajalin mutum Idan ba a gaggauta neman maganin ba.

Cutar ta yi ajalin mutum sama da 400,000 a yanki Kudu da Saharan Afrika.

A Najeriya cutar ta zama annoba inda a shekara mutum miliyan 53 na kamuwa da cutar sannan cutar na yin ajalin mutum 81,640 a shekara.

KARANTA:  Akalla maza 194 ne mata suka ci zarafin su cikin watanni shida a jihar Legas

Kasashen duniyan da har yanzu suke fama da yaduwar Zazzabin cizon sauro sun Fara sa ran rabuwa da cutar kwata-kwata saboda labarin hada maganin rigakafin cutar da suka ji.

WHO ta ce a yanzu haka ingancin maganin ya kai kashi 75% sannan idan komai ya tafi daidai za a fara amfani da maganin rigakafin a kasashen Afrika.

Gidajen sauro

Minista Ehanire ya ce gwamnati ta raba gidajen sauro sama da 17 a wasu jihohin kasar nan.

Ya ce yin haka na Daya daga cikin matakan dakile yaduwar cutar nan da shekaran 2030 da gwamnati ta dauka.

Shugaban kamfanin ‘Vestergaard’ Michael Joos ya ce raba wa mutane gidajen sauro na cikin manyan hanyoyin da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Ya ce idan har mutane na amfani da gidajen sauro a gidajen su duk wani matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati ta dauka zai zama da sauki wajen zantar da su.

Joos ya kuma koka da rashin ingancin gidajen sauron inda ya yi kira ga gwamnati da ta samar da ingantattun gidajen sauro domin kare lafiyar mutane.

KARANTA:  Masarautar Katsina ta dakatar da Hakimin Kankara, saboda zargin mu’amala da ’yan bindiga

Ware kudade domin yaki da zazzabin cizon sauro

Kungiyar WHO ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ware kudade domin ganin an yaki zazzabin cizon sauro a kasar nan.

WHO ta ce inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasan domin Samar wa mutane kula ta gari a farashi mai sauki na cikin bangarorin da ya kamata gwamnati ta fi bada karfi a kai.

Kungiyar ta ce wasu kasashen duniya 24 sun samu nasaran yaki da cutar a kasashen su inda 11 daga cikinsu sun samu takardun shaidan rabuwa da cutar kwata-kwata a kasashen su.

Wadannan kasashe kuwa sun hada da Daular Larabawa, Morocco, Turkmenistan, Armenia, Sri Lanka, Kyrgyzstan, Paraguay, Uzbekistan, Algeria, Argentina da El Salvador.

Wadannan kasashe sun samu nasaran rabuwa da cutar ne a dalilin namijin kokarin da Suka yi shekaru da dama da suka gabata.