GARKUWA DA MUTANE: Amurka ta gargadi ‘yan kasar ta su kaurace wa jihohi 15 a Najeriya

Cikin wata sanarwa mai cike da gargadi da shawarwari, gwamnatin Amurka ta gargadi ‘yan kasar ta da ke Najeriya su kaurace wa wasu jihohi 15, wadanda sanarwar ta ce ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane na ci gaba da kara muni.

Sanarwar wadda Ofishin Harkokin Jakadun Amurka ne ya wallafa ta a ranar Talata, ta yi nuna da cewa ana kara samun lalacewar al’amurran tsaro a wasu jihohi, inda ta’addanci da garkuwa domin karbar kudaden fansa ya kara muni sosai.

“Ku yi kaffa-kaffa tare da kaurace wa jihohin da tashe-tashen hankula irin su garkuwa da mutane, ta’adanci, fashi cikin ruwa da sauran laifuka su ka yi katutu.” Inji sanarwar.

“Kada wanda ya kuskura ya je Barno, Yobe, Arewacin Adamawa, Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Zamfara saboda garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya yi muni matuka.

“Kuma kada wanda ya kai kan sa jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta da kuma Ribas.

“Ana gargadin masu katin zama da kasa biyu, wato Amurka da Najeriya, idan sun zo Najeriya, to su guji wadannan jihohi saboda matsalar masu yin garkuwa da mutane domin a biya su kudin fansa.

KARANTA:  Twitter ta cire kalaman da Buhari ya yi wa 'yan IPOB barazanar gwamnati zata maida musu da niyar su ta yadda za su fi' ganewa'

“Su ma gangariyar Amurkawan da ke shigowa Najeriya, su yi kaffa-kaffa, domin masu garkuwa na yi masu kallon kudi idan sun damke su.” Inji sanarwar.