TALLAFIN KORONA: Yadda ‘yan siyasa su ka yi watandar hakkin marasa galihu a Kano, Lagos, Neja da wasu jihohi – BudgiT

Kungiyar bin Diddigin Yadda Ake Gudanar da Ayyukan Gwamnatoci Bisa Gaskiya da Adalci, mai suna BudgiT, ta bayyana damuwa dangabe yadda aka raba kudaden tallafin korona a Najeriya.

A cikin wani Rahoton Bincike kan Yadda aka Kashe Kudin Tallafin Korona, BudgiT ta bayyana yadda ’yan siyasa su ka karbe ragamar rabon tallafin korona, su ka cinye rabo da hakkin talakawa masara galihu a wasu jihohin kasar nan.

“Babban misali a nan, a ranar 7 Ga Afrilu, 2020, COCAVID wadda gamayyar kungiyar masu bada tallafi ce, ta karbi gudummawar tallafin kudade naira biliyan 21.5 kamar yadda PROSHARE BUdgiT ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Lagos: An Maida Kayan Tallafi Zuwa Kayan ’Yan Jam’iyya:

BudgiT ta bayyana cewa rahotanni da kuma binciken gani da ido da kungiyar ta gudanar a mafi yawan kananan hukumomin Jihar Lagos, musamman a Agege, Mushin, Ikorodu. Surulere da Epe, duk ‘yan siyasa ne su ka karkatar da rabon ga kan su da kuma ‘yan jam’iyyar su.

“Da yawan mutanen da ba ‘yan jam’iyya mai ci ba sun nuna damuwa dangane da yadda aka karkatar da kudade da kayan tallafi ga ‘yan jam’iyya maimakon duk wani marasa galihu mai rabo.

KARANTA:  Ban ɗauki nauyin harin da aka kai garin Igangan, inda aka kore ni ba -Sarkin Fulanin Igangan

Shugabannin Mazabun Jam’iyya Su Ka Raba Tallafin Korona:

“An rika damka aikin rabon kayan tallafi ga shugaban jam’iyya a mazabu cikin Karamar Hukumar Agege a Jihar Lagos.

“An rika raba mudun shinkafa daya da mudun wake daya da kuma ledar tumaturin keda daya ga layi daya mai gidaje sama da 30.”

“A lokacin tarzomar #EndSARS, matasa sun fasa rumbun ajiyar kayan abincin tallafin korona da aka ki rabawa a lokacin kullen korona, a unguwar Maza-maza da ke cikin Karamar Hukumar Ojo, a Jihar Lagos.”

BudgiT ta ce irin yadda aka yi a Jihar Lagos haka aka yi a wasu jihohin kasar nan da dama, inda ‘yan siyasa su ka karbe ragamar rabon abincin tallafin korona.

Kano: Yadda ’Yan Jam’iyya Mai Mulki Su Ka Manta Da Marasa Galihu A Minjibir -BudgiT

Kungiyar BudgiT ta bayyana cewa binciken ta ya tabbatar mata cewa a Jihar Kano a Karamar Hukumar Minjibir, an rika raba kayan abincin tallafin a tsakanin ‘yan jam’iyya su ya su, aka yi biris da marasa galihun da domin su aka bayar da tallafin.

Tallafin Korona Sai Mai Katin Jam’iyya:

“An umarci shugabannin jam’iyya su rika raba kayan abincin tallafin korona ga ‘yan jam’iyya kadai su ya su. Kuma ko a cikin su din, sai wanda ya nuna katin shaidar cewa shi dan jim’iyya ne.” Haka rahoton ya bayyana.

KARANTA:  'Yan BINDIGA: 'Yan sanda biyu sun rasu, mahara da dama sun sheka lahira a Zamfara

Irin yadda aka yi Minjibir cikin jihar Kano, haka aka yi a wasu wurare, kuma haka aka rika yi a Jihohin Ogun, Ribas, Neja da wasu jihohi da yawa.

BudgiT ta bayyana cewa a ranar 7 Ga Afrilu, 2020, CACOVID ta karbi tallafin kudaden gudummawa daga kamfanoni da cibiyoyi har naira biliyan 21.5 domin sayen kayan abinci a raba wa marasa galihu.

“Amma har yau din nan da mu ka fitar da bayanan abin da mu ka bankado, ba a bayyana sahihiyar hanyar da aka kashe kudaden ba domin wanda ke da shakku ya gamsu, ya daina tababa. Dalili kenan mu ke cike da nuna damuwa cewa ba a yi rabon kayan abincin tallafin korona ‘bil-hakki-da-gaskiya’ ba.

BudgiT ta yi amfani da binciken da ta yi a jihohin Niger, Lagos, Kano, Ogun, Enugu da Rivers, wanda ta ce hakan ya tabbatar mata cewa ta kasa gano takamaimen marasa galihun da aka ce an raba wa kayan abincin tallafin.