APC ta cika duka alkawaruran da ta dauka kafin samun mulkin Najeriya – Dan majalisa Yusuf Gagdi

Shugaban kwamitin sojojin ruwa na majalisar wakilai Yusuf Gagdi ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta cika wa ‘yan Najeriya duka alkawuran da ta dauka a lokacin kamfen.

Gagdi ya fadi haka na lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Ya ce abinda yasa mutane ke ganin ko akwa wani abu da gwamnatin ba ta yi ba shine kawai na rashin kurarin abin fadi wa ‘yan Najeriya dinbin abubuwan da suka yi.

“Ni na san matsalolin da kasar nan ke ciki kafin Buhari ya hau mulki, kuma na ga irin canjin da aka samu.

“Babu yadda za a yi ka kwatanta gwamnatin yanzu dake siyar da gangan mai daya akan dalla 22 da gwamnatin baya da ta rika siyar da gangan mai daya akan dalla 100 ba.

Gagdi ya ce wata matsalar da ke ci wa gwamnatin nan tuwo a kwarya shine rashin masu ba gwamnatin shawara ta kwarai.

Amma duk da haka gwamnatin Buhari ya yi kokari wajen samar wa mutane ababen more rayuwa.

KARANTA:  Wasu na zargin cewa yarjejeniyar da ta tanadi dunkule Najeriya a matsayin kasa guda a shekarar 1914 ta kare bayan shekaru 100. Shin hakan gaskiya ne? Binciken DUBAWA