HARAJI: KADIRS ta garkame ofisoshin gudanarwar hukumar wutar lantarki ta Kaduna

Hukumar tara kudaden Haraji tabjihar Kaduna KADIRS ta garkame babban ofishin wutan lantarki na jihar Kaduna wanda ke kan babban titin Ahmadu Bello dake Kaduna.

Bayan babbar hedikwatar da hukumar ta kulle, ta bi sauran ofisoshin hukumar da ke NDA, Unguwan Dosa da kwayen Kawo duk ta garkame su saboda kin biyan haraji.

Gwamnatin Kaduna na bin hukumar wutar lantarki na jihar Kaduna bashin naira miliyan 464. 5 kudin harani da bata biya ba.

Sakataren hukumar kuma lauya, Aysha Mohammed ta ce hukunar ba ata biyan kudin harajin ma’aikatanta na PAY AS YOU EARN, sannan kuma ta na bin hukumar bashi kudin baraji da bata biya ba tun daga 2012 zuwa 2018.

Aysha ta ce hukumar KADIRS ta yi ta bin hukumar da tattaunawa da su amma suka toshe kunnuwarsu suka yi banza da hukumar.

Akarshe dai hukumar ta ce ba za asake bude ofisoshin ba sai an biya wadannan kudade da jihar ke bi bashi.

KARANTA:  Lale-lale maraba da zuwa APC gwamna Matawalle - Tsohon gwamna Yari