Abuja Hausa Labarai News PREMIUM TIMES Rahotanni

Yadda mayakan ‘yan tawaye suka kashe Idris Deby na Chadi bayan shekaru 30 ya na mulkin kasar

Written by Tabarau

Shugaban kasar Chadi da ke makwabtaka da Najeriya ya rasu bayan shekaru 30 da yayi yana mulkin kasar.

Mayakan tawaye suka kasbe Deby bayan samun sa da aka yi da harsahi a filin daga.

Shugaban da kansa ya jagoranci rundunar sojojin kasar fafatawa da mayakan da ke tawaye a yankin Arewacin kasar.

Idan ba a manta ba, Deby ya sake lashe zaben shugaban kasar Chadi a karo na 6 a zaben da aka yi a kasar a cikin watan Afirilu.

BBC Hausa ta ruwaito cewa tuni dai an rusa gwamnati da majalisar dokoki, sannan majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18.

A ƙarshen makon jiya ne ya dira filin daga tare da sojojin kasar don kai wa dakarun sojoji da ke yaƙi da ƴan tawaye ziyara.

Sannan kuma ko a ranar zaben da aka gudanar a kasar wata ƙungiyar ƴan tawaye ta kai hari Chadi daga sansaninta da ke Libiya.

Ƴan tawayen sun tunkari Ndjamena fadar gwamnatin ƙasar har suka yi kurarin cewa ta ƙwace wani babban yankin babbar birnin.

Shugaban ƙasar, wanda ya sha tunkarar ƴan tawaye a cikin shekaru talatin ɗin da ya shafe yana mulki, ya tafi har arewaci don yaƙarsu. Bayan barin wuta da aka yi babu kakkautawa, Deby ashe ajali ya yi.

KARANTA:  Pillars ta ɗare saman Tebur bayan lallasa Eyimba da ta yi da ci 2-1 a Kano

Ya cika a asibiti, kamar yadda sojojin suka sanar a kasar.

Leave a Comment