Abuja Africa Chadu Deby Hausa Labarai Mahamat News PREMIUM TIMES

Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya gaji mahaifin sa, an nada shi shugaban kasar Chadi

Written by Tabarau

Majalisar Koli ba sonojin kasar Chadi ta nada dan marigayi Idris Deby, sabon shugaban kasar Chadi na riko.

BBB Hausa ta ruwaito cewa bayan wannan nadi an saka sabbin dokoki a kasar da suka hada da rusa majalisa da rufe kan iyakokin ƙasar.

” Kafa dokar hana fita a faɗin ƙasar wacce za ta fara aiki daga ƙarfe shida na yamma zuwa biyar na safe.

Rasuwar shugaban kasar Chadi, Idris Deby

Shugaban kasar Chadi da ke makwabtaka da Najeriya ya rasu bayan shekaru 30 da yayi yana mulkin kasar.

Mayakan ‘yan tawaye suka kashe Deby bayan samun sa da aka yi da harsahi a filin daga.

Shugaban da kansa ya jagoranci rundunar sojojin kasar fafatawa da mayakan da ke tawaye da gwamnatinsa a yankin Arewacin kasar.

Idan ba a manta ba, Deby ya sake lashe zaben shugaban kasar Chadi a karo na 6 a zaben da aka yi a kasar a cikin watan Afirilu.

BBC Hausa ta ruwaito cewa tuni dai an rusa gwamnati da majalisar dokoki, sannan majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18.

KARANTA:  An damke wanda ya yi 'kashin' kullin hodar Ibilis 59 a filin jirgin saman Abuja

A ƙarshen makon jiya ne ya dira filin daga tare da sojojin kasar don kai wa dakarun sojoji da ke yaƙi da ƴan tawaye ziyara.

Sannan kuma ko a ranar zaben da aka gudanar a kasar wata ƙungiyar ƴan tawaye ta kai hari Chadi daga sansaninta da ke Libiya.

Ƴan tawayen sun tunkari Ndjamena fadar gwamnatin ƙasar har suka yi kurarin cewa ta ƙwace wani babban yankin babbar birnin.

Shugaban ƙasar, wanda ya sha tunkarar ƴan tawaye a cikin shekaru talatin ɗin da ya shafe yana mulki, ya tafi har arewaci don yaƙarsu. Bayan barin wuta da aka yi babu kakkautawa, Deby ashe ajali ya yi.

Ya cika a asibiti, kamar yadda sojojin suka sanar a kasar.

Leave a Comment