Abuja Babban Labari Ja'afar Labarai Najeriya News PREMIUM TIMES Rahotanni

GANDUJE: Zargin karbar cin hancin Daloli: ‘Yan sanda na farautar Ja’afar Ja’afar

Written by Tabarau

Mawallafin Jaridar Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na neman sa ruwa a jallo ne saboda ya bidiyon da ya wallafa na karbar cin hanci daloli da aka nona gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karɓa.

A wata wasika da rundunar ‘yan sandan kasa suka rubuta wa Ja’afar, ta hannu A.A Elleman, dake ofishin Sufeto Janar din Najeriya, rundunar na bukatar Ja’afar ya bayyana a hedikwatar rundunar ƴan sandan kasa, a Abuja domin yin bayani game da wasu korafi da aka shigar a kan sa.

Wadandan korafe-korafe kuwa sun haɗa da, ɓata suna, yin zagon ƙasa, shirga ƙarya da neman ingiza mutane su tada husuma da keta wa ofishin sufeto janar din ƴan sandan Najeriya rashin mutunci wanda aka samu yana da hannu a ciki.

” A dalilin haka rundunar ya ke bukatar mawallafin jaridar ya bayyana ofishinta domin amsa wasu tambayoyi akan wadannan Zargi.

Sai dai kuma tuni , Ja’afar ya yi layar zane, inda ya shaida cewa dole yayi haka domin kansa da iyalan sa.

” Ba bu abinda ya hadani da sufeto janar din ƴan sandan Najeriya, ban taba wani rubutu akan sa ba na batanci ko tun a baya ma. Rufa-rufa kawai ake yi min wanda idan na bayyana sai su damke ni.

KARANTA:  Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya, sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, COAS

Idan ba a manta ba jaridar Daily Nigerian ce ta fara wallafa wasu bidiyo da ke nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karkacewa ya na cusa bandir din daloli a aljufan kaftanin sa.

Ana zargi wadannan kudade da gwamna Ganduje ke karbar su daga hannun wani dan kwangila ne da ya ke mika masa kason sa na cin hanci.

Leave a Comment