Abuja Hausa Labarai Labarai daga Jihohi Najeriya News PREMIUM TIMES

Rundunar tsaron yankin Yarabawa, Amotekun ta kama shanu 250 da ake zargin sun barnata gonaki a jihar Ondo

Written by Tabarau

Rundunar Tsaron yankin jihohin Yarabawa, Amotekun ta kama shanu 250 da ta ke zargi da barnata gonaki a gonaki da dama a fanin jihar.

An kama wadannan shanu ne a garuruwan Ipogun, Ilara, Owena Dam da ke karamar hukumar Ifedore, jihar Ondo.

Kwamandan Amotekun na jihar Ondo, Adetunji Adeleye ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Adeleye ya shaida cewa ko da ya ziyarci gonakin da shanun suke lalata ya iske wasu a wurin suna barnata kayan gona ba su tafi ba.

” A wasu gonakin ma ba shanun ne ke hakar doya, rogo da gwazan da aka shuka ba suna ci, makiyayan da kan su ke hako musu abincin suna baiwa dabbobin suna ci.

” Haka kuma, a wani gonan mun iske makiyayan tsaye suna jiran mu. Mu yi kokarin afka mana amma daga bay sai suka arce. Mun kama shanu 250.

Channels TV wanda ita ce ta ruwaito wannan labari ta ce a karshe an sa hannu a wata yarjejeniya tsakanin su da manoma da rundunar domin gudun kada irin haka ya sake faruwa.

KARANTA:  Yadda ake haɗa abin sha mai daɗi da gamsarwa da Maltina cikin ɗan ƙankanin lokaci

Leave a Comment