Gobara Hausa Labarai Labarai daga Jihohi Najeriya News PREMIUM TIMES

KWARA: Gobara ta cinye shaguna 30 a kasuwar Oro

Written by Tabarau

Jami’an Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta bayyana cewa gobara ta babbake shaguna 30 a kasuwar Ore dake karamar hukumar Irepodun.

Kakakin hukumar Hassan Hakeem ya ce gobarar ta auku ne dalilin kona bolan da mutane ke yi a kasuwar.

” Gobarar da ta fara ci da karfe 3 na yammacin Litinin ta lashe shaguna 30 daga cikin shaguna 354 da ake da su a kasuwar.

Shugaban hukumar Falade Olumuyiwa ya ce ya za a ci gaba da wayar wa mutane kai game da illar cinna wuta a kasuwanni kamar haka.

Gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnati za ta tallafa wa wadanda gobarar ta yi wa ta’adi.

Ya kuma ce gwamnati za ta gyara babban asibitin Oro domin mazauna kauyen sun samu ingantaccen kiwon lafiya.

A ranar 4 ga Afirilu, gobara ta kona kasuwar da ake sayar da kayan motoci da babura kurmus a Agodi-Gate, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Gobaran ta tashi ne bayan an maido wutar lantarki cikin dare.

KARANTA:  Da gaske ne wasu shanu sun ci guba sun mutu a Ondo kamar yadda a nuna a wasu hotuna? Binciken DUBAWA

Leave a Comment