Abuja Babban Labari Hausa Labarai Najeriya News Pantami PREMIUM TIMES Rahotanni Sheikh

ALAKA DA BOKO HARAM: Shin da gaske ne kasar Amurka ta balla wa sheikh Pantami hasken wutan zargi

Written by Tabarau

A ranar 12 ga Afirilu wata jarida mai suna Independent ta wallafa labarin cewa wai kasar Amurka ta sa wa Sheikh Ibrahim Pantami ido kan zargin sa da alaka da kungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce wai hukumar tsaro na sirri a Amurka ta na bibiyar ayyukan sa sau da kafa a dalilin wannan zargi.

Haka kuma a wani zargin, wani dan jarida mai zaman kansa, David Hundeyin ya saka wani bodiyon dake nuna Pantami da sheikh Yusuf a lokacin da suke wani mukabala mai zafi, wand shi Pantami ke kalubalantar wannan akida ta kungiyar Muhammed Yusuf.

PREMIUM TIMES ta gudanar da binciken kwakwaf inda Yusuf Akinpelu ya bi diddigin wadannan rahotanni da kuma bayannan domin binciko gaskiyar abinda yake game da wannan zargi da korafi.

Da farko dai babu wata hujja da aka bayar cewa wai Amurka na bibiyar sheikh Pantami, wai har sun kyallara masa haske ta musamman bisa zargin wai yana da alaka da Boko Haram a Najeriya.

Haka kuma ita kanta inda jaridar da ta wallafa wannan labari ta shirga karya ne cewa wai ta samo shi a wani taska ce ta sirri, bincike ya nuna cewa babu irin wannan taska ko kuma kundin labarai kamar yadda ita jaridar ta ce a nan ta kwakulo hujjojinta.

KARANTA:  TSAMOWA KO TSOMAWA?: Tsamo mutum miliyan 10.5 daga ƙangin talauci da Buhari ya ce ya yi, akwai lissafin-dawakan-Rano a kalaman -Bincike

Tuni dai jaridar ta cire wannan labari daga shafinta.

Haka kuma wannan bidiyo da aka rika yadawa dake nuna sheikh Pantami da Muhammad Yusuf wai suna zaman nishadi na abokantaka shima karya ne.

Wannan bidiyo bidiyo ne da ke nuna Pantami a lokacin da muke mukabala mai zafi tsakaninsa da Muhammed Yusuf.

A wannan mukabala, sheikh Pantami na kalubalantar Muhammad Yusuf tare da bashi wasu hujjoji masu karfin gaske game da inganci karatun Boko a Musulunci wanda manyan malamai da dama a duniya suka yi ittifaki akai cewa ya hallata.

Amma kuma wasu suka karkatar da ma’anan wannan bidiyo saboda wata manufa tasu suka yi mata mummunar fassara saboda wani mummunar ra’ayi na su.

PREMIUM TIMES ta nemi bayanai daga bakunan mawallafan jaridun da suka wallafa wannan labarin kage domin ji ta bakunan su amma duk sun ki cewa komai akai, duk wanda muka nemi ya ce wani abu sai ya sulale ya ce zai nememu gaba kadan.

Sannan kuma ita kanta ma’aikatar tsaron Amurkan da suka ce wai sune suke zargin Pantami da alaka da Boko Haram, babu ita kwata-kwata a jerin hukumomi da ma’aikatun tsaron Amurka, karya ce kawai da kagen iska.

KARANTA:  RAYUWA ‘BA TABBAS’: Yadda ta kaya tsakanin Shehu Sani da korarren ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna

A karshe dai abinda muka gano bayan bincike da PREMIUM TIMES ta yi tundaga nan gida har zuwa can Amurka din domin tantance gaskiyar wannan zargi, ta gano ita kanta kasar Amurkan ma bata san da labarin ba, sannan babu wani abu na zargi da ya hada wata hukumar tsaron kasar da Pantami. Kuma wannan hukuma da aka ce wai ita ce ke bibiyar Pantami babu hukuma irin haka a kasar Amurka.

Leave a Comment