LAKANIN CUTAR KORONA: Hukumomin Kula da Lafiyar Amurka sun ce a tsaida dirka wa mutane rigakafin Johnson & Johnson

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Bazuwa ta Amurka (CDC) da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Amurka, sun bada shawarar a gaggauta daina dirka wa mutane allurar rigakafin korona ta kamfanin Johnson & Johnson.

Wannan shawarar gaggawa ta biyo bayan rahotannin tabbacin samun matsalar daskarewar jini da toshewar magudanan jini da wasu mutum shida su ka fuskanta, bayan an dankara masu allurar.

Wannan lamari ya zo ne a Amurka, bayan wasu kasashe da dama, akasari na Turai sun dakatar da dirka wa al’ummar kasashen su allurar rigakafin korona samfurin AstraZeneca, bisa dalilan matsalar daskarewar jini da kuma toshewar magudanan jini da wasu da aka yi wa allurar su ka rika fuskanta.

PREMIUM TIMES HAUSA ta rika buga labaran yadda kasashen suka rika guje wa rigakafin na AstraZeneca, daidai lokacin da a nan Najeriya ake ci gaba a dankara wa mutane sinadarin rigakafin na AstraZeneca.

A ranar Talata ce Mataimakiyar Daraktar Cibiyar CDC ta Amurka, mai suna Anne Schuchat, tare da kuma Mataimakin Daraktan Cibiyar FDA, Peter Marks, su ka fitar da wannan sanarwa da kuma shawara.

KARANTA:  Sake nazarin dokokin Najeriya bata lokaci ne kawai - Afe Babalola

Wadanda su ka fuskanci matsalar daskarewar jini da toshewar magudanan jinin kamar yadda hukumomin Amurka su ka tabbatar, akwai matasa masu shekaru daga 18 zuwa magidanta masu shekaru 48.

Sanarwar ta kara da cewa mutanen shida sun fuskanci wadannan alamomi ne bayan kwanaki 13 da dankara wa kowanen su allurar rigakafin cutar korona ta Johnson & Johnson.

Tuni dai aka dankara wa sama da mutum miliyan 6.8 rigakafin Johnson & Johnson a matsayin lakanin korona.

Sanarwar ta kara da cewa za a kira taron gaggawa na Kwamitin Shawara kan Allurar Rigakafi (ACIP) a ranar Laraba, domin sake nazarin wadanda su ka kamu da matsalar ta daskarewar jini da toshewar magudanan jini, ta yadda za a san ko matsalar ta yi masu illa sosai.