Abuja Hausa Labarai Labarai daga Jihohi Najeriya News PREMIUM TIMES Uba Sani

AZUMI: Ina taya ‘yan uwa musulmai murnar zagayowar watan Ramadana – Sanata Uba Sani

Written by Tabarau

Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya hori musulmai su dage da yin addu’o’i wa kasa Najeriya da kuma yi wa al’umman musulmai fatan Allah yasa a yi Azumin watan Ramadana lafiya.

Sanata Sani ya bayyana cewa wannan watan rahama wata ce da dukka musulmai suke dukufa wajen tsananta bauta zuwa ga Allah da kuma yin addu’o’i.

” Muna fatan za a fara Azumi lafiya a kuma ga lafiya. Allah ya kara mana zaman lafiya a kasa baki daya da jihar mu, jihar Kaduna.

” Ina yin kira da godewa mutanen mazabar Kaduna Ta Tsakiya bisa goyon bayan da suke bani a agtsayin sanatan su da kuma mutanen jihar Kaduna gaba daya.

“Allah ya sada mu da dukkan Alkhairan dake cikin wannan wata na Ramadana”

A karshe ya yaba wa irin ayyukan ci gaba da gwamnatin Nasir El-Rufai ke aiwatarwa a fadin jihar.

KARANTA:  Yadda ake ta shirga karya da sunana wai an mallaka min fili na alfarma a Kaduna - Kadaria

Leave a Comment