GOBARA A PDP: An ba hammata iska tsakanin magoya bayan Kwankwaso da Tambuwal a Kaduna

Magoya bayan jam’iyyar PDP sun ba hammata iska a wurin zaben shugabannin Jam’iyyar na yankin Arewa Maso Yamma da aka yi a Kaduna ranar Asabar.

Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan jiga-jigan Jam’iyyar biyu sun kaure da fada bayan sun ki amincewa da juna bisa yan takarar da aka tsayar.

Kwankwaso na zargin gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal da yi wa jam’iyyar katsalandan a ayyukan ta a Kano.

An zo wurin zabe tiryan tiryan sai fada ya kaure, aka bi akwatinan aka farfasa, sannan aka kekketa takardun zaben, taro ta tarwatse.

Yanzu dai ba a san halin da ake ciki ba sai an saurari jawabi daga uwar jam’iyyar don sanin ina aka dosa.

KARANTA:  GARKUWA DA MUTANE: Sace-sacen ya isa haka nan, ba mu iya barci idon mu rufe - Mazauna Suleja, Garaku