TAKARA 2023: Ban taba shaida wa kotu cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne – Malami

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya ce shi fa bai shigar da wata kara ko umarnin kotu ta dauki mataki kan ikirarin cewa tsohon Matamakain Shugaban Kasa Atiku Abubakar, bad an Najeriya ba ne.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Minista Malami, mai suna Umar Umar Gwandu ya saw a hannu, Ministan Shari’a ya ce, “Abin bakin ciki ne da takaici wasu su tsuguna su ka watsa labarai na shekarun baya can, sannan su rika jirkita su, tamkar labaran kwanan nan ne, su na bugar da hankulan jama’a.” Inji Minista Malami.

“To ni dai ban taba shigar da wata shaida ko hujja ko furuci a kotu cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ba dan Najeriya ba ne” Inji shi. Atiki bad an Najeriya ba ne.

Wasu kafafenyada labarai, banda PREMIUM TIMES sunbuga labari cewa Malamai ya taba aika wa wata kutu a Najeriya duk da Atiku dan Najeriya ne, amma ba cikin Najeriya aka haife shi ba, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.” Wannan kalamai Malami y ace baib taba yin wannan kasa ba.”

KARANTA:  SULHU DA YAN BINDIGA YA KARE : Matawalle ya bada umarni a bude wuta ga duk wanda aka gani da makami a Zamfara

Malami ya ce bai taba yin wannan magana ba a kotu ko a wani wuri ba.

An ce Malami ya ce “Atiku bai cancanci tsayawa takarar shugabancin kasa a wancan lokacin ba, wato 2019, saboda a lokacin da aka haife shi, yankin garin su a karkashin kasar Kamaru ya ke, ba karkashin yankin Adamawa cikin Najeriya ba.”

Malamai ya ce bai taba bayyana wa kotu wannan magana ba ko a mafarki.