Ministan Gona Nanono ya angwance da ‘yar shekara 18

Ministan Ayyukan Gona da raya karkara Sabo Nanono, ya aure yarinya ‘yar shekara 18 da haihuwa a garin Jere dake Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Nanono, mai shekara 74, ya auri Rakiya mai shekara 18 cikin sirri inda mutum uku ne kacal suka yi masa wakilci a wajen daurin auren.

Auren dai ya haifar da cecekuce duk da cewar bai sabawa shari’a ba, amma an ce ana barin halal dun kunya in ji Hausa.

Amarya Rakiya harma ta tare a dakinta dake gidan ministan a Kano, inji Jaridar Daily Nigerian.

Jaridar tace ankai ruwa rana tsakanin minista Nanono da iyalan gidansa wadanda suke adawa da auren yarinyar mai karancin shekaru idan aka kimanta shekarun sa.

Jaridar ta ruwaito cewa minista Nanono ya ya wa wakilan sa kunne su tabbata ba su fallasa wannan aure ba, sai dai abinka da abinda ya wuce mutum daya, tuni labarin auren ya karade duniya.

Wani da ya ce a sakaye sunan sa domin gudun tsangwama ya bayyana cewa, Rakiya mai shekaru 18 ta yi kanekane a zuciyar Minista Nanono, ita ce kawai ya ke gaban sa saboda tsaninin so da yake mata har zuwa ya aureta a asirce.

KARANTA:  HATTARA 'YAN TALLA: Matsafi ya guntule kan ’yar tallar shinkafa da miya

Dyk da iyalan sa ba su so hakan ba, aikin gama ya gama, Nanono ya angon Rakiya, tana ma gidan dakinta ta na cin amarcin ta hankali kwance.