Allah yayi wa Hon Suleiman Aliyu Lere Rasuwa

Da safiyar Talata ne Allah yayi wa dan majalisan dake wakiltan Lere a majalisar Wakilai ta Tarayya rasuwa.

Honarabul Suleiman Aliyu Lere ya rasu a asibitin Barau Dikko da ke garin Kaduna bayan fama da yayi na rashin lafiya.

An rantsar da Suleiman Aliyu dan majalisa a cikin watan Maris baya shekara biyu da yayi yana kotu wajen Kalubalantar zaben kujerar dan majalisan tsakanin sa da Lawal Adamu na Jam’iyyar PDP.

Kotu a farkon shekarar nan ta yanke hukuncin Honarabul Aliyu ne yayi nasara a zaben da aka yi ta kai ruwa rana akai.

Yan uwan da abokan arziki duk sun dunguma zuwa garin Lere domin halartar jana’izar sa.

Premium Times Hausa na taya iyalan jimamin wannan rashi.

Allah ya ji kan sa Amin.

KARANTA:  Ƴan bindiga sun sace malamai da ɗaliban Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zariya