Wani gwamna ya yi barazanar fallasa masu cusa siyasa a lamarin tsaro

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi barazanar fallasa masu cusa siyasa a lamarin tsaron jihar Oyo.

Makinde ya yi wannan barazana ce a lokacin da ya ke jawabi ga taron gangamin mabiya addinin Kirista a Cocin St Preters Anglican Cathedral da ke Aremo, Ibadan a taron Easter ranar Lahadi.

Gwamnan ya yi duk da jihar Oyo na fuskantar matsalar tsaro, to amma matsalar ba a jihar sa kadai ta tsaya ba, abin ya zama ruwan dare a fadin kasar nan.

Cikinn wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran Gwamna Makinde, mai suna Taiwo Adisa ya fitar kuma ya sa wa hannu, Gwamnan na Oyo ya bayyana cewa bai dace ba kwata-kwata a tsarma siyasa a lamarin tsaro.

Ya kara da cewa, “to amma idan su ka cusa siyasa ne a lamarin tsaro domin su hau mulki a zaben 2023, to su sani cewa su na tabka babban kuskure.”

Makinde ya ce gwamnatin sa ta dauki lokaci wajen bincike da kuma kokarin kawo mafita ga matsalar tsaro, a cikin wani rahoton tsaro a fadin jihar.

Daga nan sai ya gargadi maso amfani da siyasa su na cuwa ta a cikin namarin tsaron kasar saboda zaben 2023, to koma ga Allah, idan ba su yi hakan ba kuwa, to za su haifr da rudani da tsaro ne a zukatan al’ummar jihar Oyo.

KARANTA:  Yadda farashin kayan abinci ya shafe watanni 10 ya na jijjiga aljifan talakawa

Makinde ya yi bayanin irin ci gaban da gwamnatin sa ta samu a cikin shekaru biyu, inda ya tabo bangarori da dama, musamman ma a bangaren tsaro.

Daga jihar Oyo ce dai guguwar korar Fulani makiyaya daga jihohin Kudu maso Yamma ta taso, inda wani gogarma mai suna Sunday Igboho ya jagoranci gungun matasa su ka fatattaki wani Sarkin Fulani bayan kone gidan sa.