'Yan Bindiga Abuja Babban Labari Bindiga Hausa La arai Labarai Najeriya News PREMIUM TIMES Rahotanni sulhu

Gwamnatin Kaduna ba ta nada kwamitin yin sulhu da ‘Yan bindiga ba, duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki

Written by Tabarau

Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi masu yayada cewa wai ta nada kwamitin yin sulhu da’ Yan bindiga a madadin gwamnatin a jihar da su shiga taitayin su tunda wuri ko kuma su yaba wa aya zaki.

A wata takarda da kwamishinan tsaron jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi, gwamnatin jihar ta karyata wannan labari da ya karade shafukan jaridu da na sada zumunta a yanar gizo.

” An jawo hankalin gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wai gwamnati ta nada kwamiti domin yin sulhu da ‘yan bindiga a jihar.

” Muna so mu shaida wa mutane cewa wannan magana babu gaskiya a cikin sa, sanna kuma tuni har gwamnati ta dana tarkon kama duk wanda sune suka kirkiro wannan abu da kuma wadanda ke da hannu wajen kirkiro kwamitin karyar.

” Matsayar gwamnatin Kaduna kan ‘ Yan bindiga na nan daram, ba za ta yi sulhu da su ba. Duk wanda yake yin haka a madadin gwamnatin jihar, ya sani ba davyawun gwamnati yake yi ba, idan kuma aka kamashi ko shi waye, Kotu za ta raba su da gwamnati.

KARANTA:  Kotu ta daure magidanci saboda satar wutan lantarki a Kano

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kaduna El-Rufai, ya fadi ya kuma kara jaddadawa cewa gwamnatin sa ba za ta biya mudin fansar wani ga mahara. El-Rufai ya ce yin sulhu da mahara ba shi bane abin yi kuma gwamnatin sa ba za ta yi haka ba.

A ra’ayin gwanma El-Rufai, a bisu inda suke a ragargaje su shine kawai mafita, amma a rika bi ana dankara musu kudi na babu gaira babu dalili, zai basu karfin guiwar ci gaba da abinda suke yi ne.

Leave a Comment