Masarautar Karaye ta koka kan kwararowar masu hakkar zinari daga Zamfara

Maimartaba Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II yayi izzina ga gwamnati kan kwararowar masu hakkan zinari daga Jihar Zamfara zuwa masarautar ta karaye dake Kano.

A baya, gwamnatin tarayya ta dakatar da hakar ma’adinai a Zamfara, tana zargin ayyukan masu hakkar ma’adinan da aikin ta’adanci na ‘yan bindiga wadda tayi sanadiyar mutuwar daruruwar mutane a wasu yankuna na arewa masu yamma.

Maimagana da yawun masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa yace msarautar ta fitar da sakon gargadi akan kwararowar masu hakkan zinari bayan taron majallissar masarautar da akayi a ranar Alhamis

Taron ya samu jagorancin sarkin na karaye Ibrahim Abubakar II wadda aka yi a fadarsa dake garin na Karaye, inji Haruna Gunduwawa.

Gunduwawa yace masarautar ta koka da cewar bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da hakkar zinari a Zamfara, wasu masu hakkar zinarin suna ta kaura zuwa yankunan dake masarautar karaye suna hakkar zinari.

Masarautar tayi kira ga jama’a da su kai rahoto kan duk wasu bata gari dake shigowa yankin na karaye da sunan hakkar zinari, inji Gunduwawa.

KARANTA:  Korona ta dawo gadan gadan: Mutum 146 sun kamu, daya ya rasu cikin kwanaki uku a Najeriya