Mutane sun shiga rudani bayan bankuna sun dakatar da siyan katin kira na MTN ta asusun banki

‘Yan Najeriya sun fada cikin halin kai komo da gararamba bayan bankunan Najeriya sun hana duk wani mai layin MTN iya siyan katin kira ta asusun ajiyar sa ta banki.

Bayan mutane sun kagara iya siyan katin kira ta bankunan su aka fara korafi da neman bayanai ta bankuna da kamfanin sadarwar MTN din sai MTN ta aika wa masu amfani da layin kiran cewa daga yanzu duk mai son kira da layin sa ta MTN ya garzaya shagunan saida kati kai tsaye da kuma kuma irin na bakin hanya ka siya katin kira.

PREMIUM TIMES ta gano cewa an samu takiya ne a tsakanin MTN da bankuna wurin raba ribar kudaden da ke cirewa idan aka siya katin.

Hakan ya sa bankunan kasar nan suka dakatar da cigaba da kamfanin MTN yanzu har sai sun warware matsalar dake tsakanin su.

Yan Najeriya da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun nuna damuwar su kan haka.

” Na shekara ya fi biyu da na siya katin kira ta hanyar siyan kati a waje. Ta waya nake yi, yau kuma gaba daya sai na rude da babu ta hanyar banki. Sai da na fita na shiga gari kafin nan na siya katin da na yi kira da shi.” inji Mohammed Nasir.

KARANTA:  Sai fa Najeriya ta daina biyan tallafin man fetur za ta iya ci gaba - Ministan Mai