Yadda Sule Lamido ya samu Jihar Jigawa a 2007, Daga Mansur Ahmad

A lokacin da Jagoran talakawan Nigeria Dr. Sule Lamido ya zama gwamnan Jihar Jigawa sauran jihohi suna kiranta da suna Ji – Gawa, domin suna mata kallon matacciyar Jiha da ta zama abar dariya da shagube a cikinsu, jihar da babu ababen more rayuwa na azo a gani.

Dalili kuwa bai wuce cewar ita ce tafi kowacce Jiha talauci a ƙasar nan ba, ita ce tafi kowacce Jiha yawan mace – macen mata a lokacin haihuwa ba, ita ce tafi kowacce Jiha yawan yara da basa zuwa makaranta, kai kusan kowanne abu na koma baya a wancan lokaci sai kaga sunan Jihar a sahun farko ko kuma a farkon ma.

Ya zama gwamna a lokacin da ɗaliban makarantun mata suke kwana a wayar ƙarfe babu ginin katanga da zata zagaye su, suke bayan gida acikin gonakan makaranta, ɗalibai maza suke kwana a ajujuwan da suke karatu da safe su ɗauke kayansu su fito dasu jikin bishiya sannan su yi karatu, ake yiwa ɗaliban makarantun kwana abincin da basa iya ci sai dai su zubar ko kuma wadda baya da abinda zai ci shine zai karba.

KARANTA:  Kungiyar Ma'aikatan Kotu sun watsa wa gwamnonin goron gayyatar janye yajin aikin da su ka aika masu

Babu inda ake karatun digiri a fadin Jihar nan, makarantun Boko babu kayan koyarwa, babu kwararrun malamai a kowanne fanni, asali ma wasu suna koyarwa amma basu da takardar shaidar koyarwa, babu kayan gwaje – gwaje babu dakunan karatu masu kyau da inganci babu walwala ga su malaman

Jihar a lokacin da ma’aikatun gwamnati suke rarrabe a kananan hukumomi barkatai, ma’aikatar Ilmi a Kazaure, ma’aikatar Ruwa a Ringim, ma’aikatar kula da noman ƙaro a Mallam Madori da sauransu, sannan babu wajen kwanan ma’aikata, babu motocin da zasu hau masu lafiya domin gudanar da aiyyukansu a cikin yanayi mai daɗi, wasu sun fi yarda su shigo Jigawa daga Kano su yi aiki sannan su koma Kano su kwana washe gari su dawo saboda babu gidajen ma’aikata in ma akwai babu gyara sun lalace.

Ya samu Jihar ana boye offer ta aikin gwamnati a inda zaka iya ganin mutum ɗaya da takardu sama da 20 yana biyan kansa albashinsu an ga misalin a ƙaramar hukumar Kaugama lokacin da yayi zagayen ƙananan hukumomi a satin farko da zamansa gwamna

Babu makarantun ƴaƴan makiya balle a damu da karatunsu ko gina musu gobensu da ta ƴaƴansu, babu kulawa ga nakasassu balle a basu tallafi ko a mayar dasu abin alfahari da za’a iya tunkaho dasu ko su ji a jikinsu cewar su ma ya’ya ne. Ya karbi Jihar Jigawa a lokacin da manyan Jihar da masu Ilmi da kwarewa a fannoni daban – daban ba’a nuna ana da buƙatar shawarwari ko gudunmawarsu dan gina jiharsu ba.

KARANTA:  MURAR TSUNTSAYE: Ciwon fakat ya fara yi wa dubban kaji kisan-kiyashi a Jihar Neja

A lokacin gwamna bai damu da zama a Jiharsa ba balle ace zai iya watanni biyu ko cikakken wata ɗaya a Jihar ba, ya samu Jihar a Lokacin da shugabanni basu da kima a idon talakawa domin in sun yi magana ba kowacce suke cikawa ba musamman in an ƙira taro ko wani bikin buɗe abu sai ace za’ayi da safe kaga dab da sallar Magarba ko Isha’i sannan ake fadawa ko ake kammalawa

Ya zama gwamna a lokacin da babu hanyoyin kwalta masu kyau hakan yasa ake yawan mutuwa sakamakon hatsari. Asibitoci babu kwararrun likitoci, ba’a damu a ɗauki nauyin yaranmu su je su yi karatu ba zai dai a daukko yan wata ƙasar su zo asibitocinmu ana biyansu, makarantunmu na lafiya babu kwararrun malamai babu kayan koyo da koyarwa na zamani.

A wancan lokacin gidan rediyon Jigawa basa iya labarai in babu wutar NEPA sai dai su je gidan mai martaba Sarkin Dutse su karbo kuɗin mai sannan a tasar da inji ayi labarai. A lokacin da ya zama gwamna a Jigawa sai ka kammala aikin gwamnati na tsawon lokaci ba’a biya ka hakkinka ba, Jihar bata damu da matasanta ba balle cigabansu ko ta fito dasu idon duniya domin a amfana da basirarsu da hikimominsu ba.

KARANTA:  Zargin Fani-Kayode cewa akwai rubutun arabi akan takardar kudin Najeriya tun kafin mulkin mallaka karya ne - Bincike DUBAWA

Ba’a damu da biyan albashin ma’aikata akan lokaci ba hakan yasa aikin gwamnati ya mutu murus misali 29 ga watan Mayu na shekarar 2007 da ya karbi rantsuwar kama aiki watan zai mutu a kwana ɗaya da zamansa gwamna amma ba’a biya ma’aikata albashi ba.

Wannan na kaɗan daga cikin yadda Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido ya samu Jihar Jigawa a shekarar 2007