Shugaban karamar Hukumar Birniwa Jaji-Dole ya rasu

Allah yayiwa shugaban Karamar Hukamar Birniwa, Muhammad Jaji-Dole, dake Jihar Jigawa rasuwa.

Maimagana da yawun karamar Hukumar ta Birniwa Sanusi Doro, ya shaida wa Premium Times Hausa, cewa marigayin ya rasu ne a daren Litinin bayan kajeriyar rashin lafiya.

Ya rasu ne a gidansa dake unguwar dolen kwana dake cikin garin ta Birniwa, Kafin rasuwarsa, yayi fama da ciwon suga, inji Doro.

Anyi jana’izarsa a garin na Birniwa da misalin karfe goma na safiyar Talata.

Marigayi Jaji-Dole ya zama zababbe Dan siyasa Wadda ya rasu kasa da wata daya a Jigawa bayan rasuwar Dan majalisa Hassan Yuguda-Kila daga Gwaram.

KARANTA:  Ministan Gona Nanono ya angwance da 'yar shekara 18