PDP ta nemi Buhari da APC su yi bayanin yadda yadda aka ‘sace’ naira tiriliyan 25 a gwamnatin su

Jam’iyyar PDP ta sake zargin jam’iyyar APC da satar naira tiriliyan 10.1 daga baitilmalin Najeriya, duk kuwa da abin da ta ke kira rashin kudin da kasar nan ke fama da shi domin yin ayyukan kasafin 2021.

Yayin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yawan korafin faduwar farashin danyen mai ne dalilin da ya sa Najeriya ke ciwo bashi, ita kuwa PDP cewa ta yi gwamnatin Buhari ta na daure wa cin hanci, rashawa da satar kudade gindi.

Cikin wata sanarwar da PDP ba ta bayyana majiya ko madogarar ta ba, kuma ba ta fayyace hujjojin zargin ta ba, ta ce akwai zargin an karkatar da naira tiriliyan 9.6 kwatankwacin dala biliyan 20 da kuma wasu naira bilyan 500 daga Asusun Bai Daya (TSA).

PDP ta ce an karkatar da kudaden ne domin biyan wata bukata ta jam’iyyar APC.

“Wadannan zunzurutun naira tiriliyan 10.1 fa daban su ke da wasu naira tiriliyan 15 da aka ce shugabannin APC sun sace daga hukumomin gwamnati daban-daban, ciki kuwa har da naira tiriliyan 9.3 da wasu takardun NNPC da aka bankado su ka nuna. Kudin sun tashi naira tiriliyan 25.1 kenan.”

KARANTA:  Minista Akpabio ya nesanta kan sa da farfesan da aka ɗaure saboda ya yi masa maguɗin zaɓe

Haka dai Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar.

Ya ci gaba da cewa irin gagarimar satar da ake yi a karkashin jami’an wannan gwamnatin, ta nuna karara cewa Najeriya ta fada a hannun wasu “yan fashin da su ka yi kane-kane a cikin manyan mukaman wannan gwamnati.”

Sanarwar ta ci gaba da nuni da cewa “gwamnatin APC na jerin sahun gaba na gwamnatocin da su ka fi lalacewa a kasashen duniya, inda kasar nan ta zama ta 149 a duniya, kamar yadda cibiyar TI ta bayyana.”

Kwanan baya sai da PDP ta nemi Gwamnatin Buhari ta yi wa ‘yan Najeriya bayanin yadda kudin makamai dala bilyan 3.5 su ka salwanta.

Jam’iyyar PDP ta kaluballanci Gwamnatin Shugaba Muhammmadu Buhari cewa ta gaggauta fitowa ta yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda dal bilyan 3.5 da aka ware domin sayen makamai su ka salwanta, tunda ba a sayo makaman ba.

Haka kuma PDP ta yi kira ga Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya su gaggauta binciken kwakwaf domin gano gaskiyar yadda aka karkatar da kudaden, da kuma wadanda su ka karkatar da su.

KARANTA:  Duk da kukan rashin kudi da gwamnati ke yi, za a kashe naira biliyan 42 a yi wa Majalisa kwaskwarima

PDP ta yi wannan kakkausan kalubale ga gwamnati da kuma kira ga majalisu ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis.

Jam’iyyar adawar ta ce sabuwar harkallar cuwa-cuwar dala bilyan 2.5 da ake zargin Mashawarcin Buhari kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno na da hannu, wanda shi ma a kwanan baya ya zargi su Buratai sun yi sama-da-fadin dala bilyan 1, sun bayyana cewa babu abin da ke wakana a karkashin gwamnatin Buhari sai masifar jidar makudan kudade.

“Ya kamata Majalisa ta gaggauta gudanar da kwakkwaran binciken gano inda aka karkatar da wadannan makudan kudaden da ya kamata a ce an sayo makamai da su domin a kare rayukan jama’a. Maimakon haka sai zargin karkatar da kudaden ke ta fitowa a karkashin gwamnatin Buhari.

“Irin yadda bangaren tsaron gwamnatin Buhari ke fallasa junan su dangane da zargin karkatar da kudaden makamai, ya nuna yadda ake tseren wuce juna tsakanin manyan jami’an gwamnatin Buhari, su na takarar wanda ya fi wani azurta kan sa da kudaden talakawan da su ka kamata a sayo makamai a kare rayukan su da dukiyoyin su.”

KARANTA:  Makaryatan ’yan siyasa ne su ka haddasa rashin tsaro da rura wutar kabilanci a Najeriya – Wani jigon APC

PDP ta ragargaji APC ta da cewa maimakon jam’iyyar ta goyi bayan talakawan kasar nan, sai ta buge da borin-kunyar kokarin kare jami’an gwamnatin da ake zargi sun yi wa junan su watandar kudaden.