Shehu Sani ya ziyarci Sheikh Gumi kan daliban Makarantan Kaduna 39 dake hannun ‘yan bindiga

Sanata Shehu Sani ya ziyarci Sheikh Ahmed Gumi domin rokon sa ya taya iyayen daliban makarantan Kaduna da yan bindiga suka sace su 39 da iya karfin sa a samu a sako daliban.

Sanata Sani ya roki shehin malamin da kada ya karaya da rashin hadin kai da ya ke samu wajen maganan sulhu da ya sa a gaba, yana mai cewa mutane a waje na yaba masa kan abin da yake yi na ganin an kawo karshen hare-hare a kasar nan.

” Na zo nan tare da iyayen daliban makarantan da aka sace domin mu roke ka idan akwai wata hanya da za abi don ganin an ceto yaran makarantan da aka sace a Kaduna a taimaka. Muna yaba maka kan kokarin da ka ke yi kafin gwamnati ta saka doka muna lallai an yaba maka.

Sai dai kuma Sheikh Gumi ya ce ba shi da karfin iya saka wa asako ko sai dai zai tai maka iya karfin sa domin ganin an samu dacewa da sako daliban.

Ya ce sai da gargadi iyayen yaran kada su kai kukan su ga gwamnati amma suka yi mishi kunnen uwar shegu su ka je.

KARANTA:  TARIN FUKA: Ci gaba da wayar da kan mutane zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar - kwararru

Idan ba a manta ba Gumi ya rika yin kira ga gwamnati ta yi sulhu da yan bindigan domin su daina sace mutane ammam suka ce ba hakan ne tsarin su ba.