El-Rufai, Saraki, Lawan, David Mark da wasu dakka sun kafa gagarimin majalisin tattauna batun sauya fasalin Najeriya

Wace hanya ce mafita daga matsalar tattalin arzikin da ta yi wa kasar nan dukan-kabarin-kishiya, ta hana kasar ci gaba? Kuma ta yaya za a iya daidaita matsalar batun sauya fasalin Najeriya, wadda ita ma ke ci gaba da ruruta tayar da jijiyoyin wuya daga bangarori daban-daban na kabilun kasar nan, har lamarin na barazanar tarwatsewar kasar nan?

Wadannan tambayoyi ne wasu shugabannin Najeriya masu hangen nesa da zurfin tunani, da masu ruwa da tsaki za su hadu a wani kasaitaccen majalisi domin su tattauna.

Za su yi tattaunawar a Lagos yayin kaddamar da wani littafi mai suna “Majalisin Tattauna Matsalolin Tattalin Arziki da Batun Sauya Fasalin Najeriya.”

Littafin dai jaridar National Pilot ce ta wallafa shi, kuma za a tattauna wadannan matsaloli biyu ne kacokan a zaman majalisin. Wato matsalar tattalin arziki da batun sauya fasalin Najeriya. Sannan kuma za su yi kokarin lalubo mafita.

Wannan ne karo na farko da za a kaddamar da littafi a kan batun sauya fasalin Najeriya, tun lokacin da wannan makabala ta samu gindin zama a cikin zukatan ’yan Najeriya.

Sannan kuma batun ya zo daidai lokacin da babu wani kokarin samar da wani lakani da aka taba yi a baya.

KARANTA:  LABARAI CIKIN HOTUNA : ƴar Kano, da dan Zamfara sun lashe gasar musabaƙar karatun alkur'ani ta kasa

Wannan kasaitaccen majalisi ya sha alwashin tattara hamshakai da mashahurai wadanda su ka yi gogayya da nuna kwarewa wajen kwance murdadden kullin igiyar da ta cukurkude tare da dabaibaye kasa ta hana ta ci gaba.

Za a gudanar da gagarimin majilisin a ranar 14 Ga Afrilu, 2021, wanda sahun farko na mahalarta akwai Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu, Ahmed Lawan, sai kuma Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, wanda zai shugabanci zaman majalisin.

Sannan kuma an gayyaci Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ga kuma Gwamna Nasir El-Rufai wanda shi ne Babban Bako Mai Jawabi.

Akwai kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti, Dapo Abiodun na Ogun, Yahaya Bello na Kogi, Nyesom Wike na Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Seyi Makinde na Oyo.

Sai kuma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas wanda shi ne Babban Mai Masaukin Manyan Baki.

Sauran wadanda aka gayyata sun hada da Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, sai Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi.

Iyayen taro a ranar sun hada da Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi shi da Mai Martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu Gambari.

KARANTA:  Shin da gaske ne 'yan fashi sun tirke wasu ma’aikatan gidan man sannan suka yi awa uku suna sayar da mai a gidan man kamar yadda aka yi ta yadawa - Binciken DUBAWA

Ana kuma sa ran halartar Are Ona Kakanfo na Yankin Yarabawa, Gani Adams. Sai tsoffin Gwamnoni irin su Olabode George, Gbenga Daniel, Ibikunle Amosun da Abdulfatah Ahmed.

Kada Ka Bari A Ba Ka Labari.