2020: Kamfanin Simintin Dangote ya yi cinikin naira tiriliyan 1 da biliyan 34, ya ci ribar naira biliyan 276 gangariya

Kamfanin Simintin Dangote, ‘Dangote Cement Plc’, kuma kamfani mafi girma a Najeriya, ya yi cinikin siminti na naira tiriliyan 1.034 cikin shekarar 2020.

Wannan ciniki da kamfanin ya yi, shi ne ciniki mafi yawa da ya taba yi a cikin shekara daya, domin bai taba yin haka a shekarun baya ba.

Cinikin shekarar 2020 ya haura na shekarar 2019 da naira biliyan 142.525.

Hakan kuma ya nuna cewa an samu riba har ta naira biliyan N373.310.

Ribar koma naira biliyan 276 ne bayan kamfanin ya ware naira biliyan 92 da zai biya gwamnatin tarayya matsayin kudin haraji.

Dangote Cement ya samu gagarimin ciniki a cikin tsakiyar shekarar 2020 ne bayan da gwamnatin Najeriya ta bude masa hanyar ci gaba da fitar da kaya zuwa kasashen Afrika ta Yamma ta kan iyakokin kasar nan, musamman Jamhuriyar Nijar da Togo

Haka dai Shugaban Ma’aikatan Kamfanin mai suna Michel Puchercos ya bayyana.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Kamfanin Simintin Dangote ya ware wa Najeriya harajin naira biliyan 97, daga cinikin shekarar 2020.

Masana’antar Dangote Cement Plc wadda ta fi kowace masana’anta sarrafa simiti a Afrika, za ta kara bunkasa tattalin arzikin Najeriya yayin da za ta damka wa Gwamnatin Tarayya harajin naira biliyan 97 daga cikin cinikin da kamfanin ya yi na siminti daga watan Janairu zuwa Disamba, 2020.

KARANTA:  Ƴan bindiga a Kudu sun ƙwace tirela cike da shanun 'yan Arewa, sun kashe direba da kwandasta a Anambara

Kiyasi ya nuna Dangote zai bayar da harajin kudin cinikin siminti na naira biliyan 97, adadin rabin kudin da Gwamnatin Tarayya ta raba wa Jihohin kasar nan 35 a cikin watan Janairu, 2021.

Kasuwar simintin Dangote ta karu sosai cikin shekarar 2020 da kashi 12.9 bisa 100, inda sayar da metric tan miliyan 15 cikin 2020.

Sannan kuma kudin shiga sun karu a shekarar 2020, inda aka kamfanin simintin Dangote ya samu kudin shiga har naira biliyan 720.

Duk da cewa an samu cikas a tattalin arzikin duniya sanadiyyar annobar korona, har yau dai Aliko Dangote ya na nan a matsayin sa na bakar fatar da ya fi kowane bakar fata kudi a duniya. Kuma wanda ya fi kowa kudi a Najeriya da Afrika baki daya.

Shugaban Ma’aikatan Dangote Cement PLC, Michel Puchersos, ya bayyana cewa, “shekarar 2020 ta yi wa Dangote Cement kyau sosai, musamman saboda sun fito da sabbin samfuran kayan da su ka samu karbuwa a Najeriya da sauran kasashe. Mun kara yawan wanda mu ke sarrafawa a Najeriya,kuma mun kaddamar da tashar samar da karfin lantarki a masana’antar mu ta siminti da ke Mtwara, Tanzania.

KARANTA:  PDP ta nemi Buhari da APC su yi bayanin yadda yadda aka ‘sace’ naira tiriliyan 25 a gwamnatin su

“Wannan kuwa ya sa bayan mun ware kudin harajin da za a bai wa gwamnati, mun samu ribar da ta kai naira biliyan 276.1” Inji shi.